Wakokin Shata Mp3 Apk Download for Android
Wannan Manhaja ta Kunshi wasu daga cikin fitattun wakon Dr. Mamman Shata. Wannan application anyi shi ne don jin dadin ku tare da fadawa yaduwar harshen Hausa a Duniya. Wakokin da ke cikin wannan Manhaja sun hada da:
*Abba Siri Siri
*ABU Zaria
*Lafiya Mamman Mai Daura
*Malam Babba Na Kofar Gabas
*Zaki Sarkin Hadejia Maje
*Umaru Dan Danduna Na Gwandu
*Sani Audi
*Gagarabadau
*Lafiya Zaki
*Na Tsaya ga Annabi Muhammadu (SAW)
*Sarkin Zazzau Shehu
*Bakandamiya
Idan kunji dadin wannan application din kada ku manta ku rubuta "review" sannana kuyi "rating" din application din, hakan zai kara mana kwarin gwiwa kuma zai habaka darajar wannan application din anan play store.
Ku duba kundin Apps dina anan playstore don samun wasu apps din masu ilmintarwa da fadakarwa, ku rubuta ZaidHBB a store sai kuyi search don ganin kundin.
Wanene Mamman Shata?
Mamman Shata wani shahararren mawakin Hausa ne wanda har duniya ta nade ba za'a sake yin kamarsa ba.Haifaffen Musawa ne ta jihar Katsina amma ya yi kaura zuwa birnin Kano. Lokacin da ya rasu an birneshi a Daura kamar yadda ya bar wasiyya. yana da wakoki wanda bicike har yanzu bai san yawan su ba dan shi kan sa an tambaye shi ko yasan adadin wakokin da yayi sai amsa dacewa bai saniba amma a shekarun baya an sami wata baturiya ta zo ta hada wakokin sa kimanin dubu hudu. yanada da abin mamaki kwarai da gaske yakanyi waka duk lokacin da aka bida yayi hakan batareda inda-inda ba.
An tambayi Marigayi Dr. Mamman Shata cewar a ina ya soma waka sai ya kada baki ya ce“A nan Musawa inda aka haife ni a nan na soma waka kuma duk inda na je yawo to da wakata suka ganni„
Ko wane dalili ya sa Dr. Mamman Shata ya soma waka a rayuwarsa, ga dai amsar da ya bayar“Dalili shine kiriniya ta yarinta kurum,bawai don gadon uwa ko uba ba, domin kuwa na dade ina yi bana kabar ko anini , in ma an samu kudi sai dai makada da maroka su dauka. Sai daga baya bayan na mai da waka sana’a na fara amsar kudi „
Shin waya sawa Dr. Mamman Shata wannan suna nasa wato Shata
“Wanda ya sa mini wannan suna Shata sunansa Magaji Salamu, shine ya samin suna Shata Mijin mai daki, ita mai dakin kaka ta ce, ita ce ta haifi wanda ya haife ni„
Da aka tambayi Dr. cewar wace waka ce ta fi suna kuma ya fi jin dadin ta ko kuma ta fi birge shi a duk ilahirin wakokin da ya yi, sai ya ba da amsa kamar haka“ To wannan wani abune mawuya ci a wurina kuma kowa yace zai iya ganewa karya yake yi tunda shi shatan bai ganeba „
---------------------------------------------------------
Category : Music and Audio App
Last Updated : 23 June, 2019
Current Version : 1.0
Requirements : 4.0+
Developer : ZaidHBB


0 Comments